1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garkuwa da mutane 30 a Zamfara

Yusuf Bala Nayaya
January 30, 2019

A cewar Falala Ashafa cikin wadanda aka kama din dai akwai matarsa da sirikarsa da wasu mambobi na iyalansu shida.

https://p.dw.com/p/3CSx4
Nigeria Sicherheitskräfte Boko Haram
Hoto: Reuters

Wasu 'yan bundiga da ba a san suwa nene ba sun yi garkuwa da mutane 30 mafi akasari mata a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya kamar yadda shedu da 'yan sanda suka bayyana a wannan Laraba.

'Yan bundigar dai sun kai hari ne a kauyen Majema a jihar Zamfara a ranar Litinin inda suka kama mata 20 da mazaje shida kamar yadda Falala Ashafa ya fada wa kamfanin dillancin labaran Jamus na dpa.

A cewar Ashafa cikin wadanda aka kama din dai akwai matarsa da sirikarsa da wasu mambobi na iyalansu shida. Ya ce maharan sun fito ne daga daji inda suka shiga kauyen suna bi gida-gida suna kama mutane. Sai dai mai magana da yawun 'yan sanda a jihar ta Zamfara Mohammed Shehu ya ce mutane 13 ne aka kama.