Garkuwa da Fira ministan Libiya | Labarai | DW | 10.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Garkuwa da Fira ministan Libiya

Fira ministan Libiya ya koma ofis bayan 'yancin da ya samu daga 'yan tawayen da suka saceshi.

Fira ministan Libiya Ali Zeidan, ya isa fadar gwamnatin kasar da ke birnin Tripoli, jim kadan bayan da mayakan da suka yi garkuwa dashi na tsawon sa'oi bakwai suka sallameshi. Ministoci da dama tare da mambobin majalisar dokokin kasar ne suka yi cincirindo domin tarbar Fira ministan, wanda ya isa fadar gwamnatin kasar cikin tsauraran matakan tsaron da ba a saba gani ba, kana ya yi ta daga hannu ga mutanen da suke babbar kofar shiga fadar. Sace fira ministan ya zo ne kwwanaki biyar bayan da wasu dakarun Amirka suka kutsa cikin Libiya domin cafke Abu Anas al-Libi da suke zargi da kasancewa mamba ne a kungiyar alQa'ida, abin da kuma ya harzuka gwamnatin da kuma 'yan kasar ta Libiya da dama.

A halin da a ke ciki kuma, sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya kwatanta sace fira ministan Libiya Ali Zeidan a matsayin wata matashiya ce game da bukatar sake yin hubbasa domin mayar da daidaiton harkokin siyasa da kuma bin doka da oda a kasar. A kan hakane sakatare janar din ya bayyana cewar, majalisar, tare da hadin gwiwar kasashen da ke makwabtaka da Libiya na taimaka mata wajen daidata sha'anin siyasa da na bin dokar. Ya kuma ankarar da shugabannin Libiya game da bukatar da ke akwai ta shirya taron sulhu da sasantawa a tsakanin 'yan kasar domin basu damar shiga cikin shirin mayar da kasar bisa turbar dimokradiyya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu