1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garkuwa da baƙi 'yan ƙasar waje a Niger

September 16, 2010

Wasu waɗanda ba'a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da ma'akatan Areva.

https://p.dw.com/p/PDqe
Ma'aikatan kamfanin ArevaHoto: DPA

Jami'an diplomasiyya da kamfanoni sun ce wasu 'yan ta'adda sun yi garkuwa da 'yan ƙasar faransa guda 5 da yan Afurka guda 2 waɗanda ke aiki a kamfanin da ke sarrafa sinadirin Nukliliya ta Areva.

Kakakin hukumar kula da harkokin wajen Faransa Bernad Valero ya faɗa a yau alhamis cewa an kama mutane bakwan ne a garin Arlit dake arewacin kasar Niger.

A wata sanarwa, valero ya shaida cewa hukumomin Faransa, shirye suke su dauki duk matakan da suka dace don shawo kan lamarin.

Wani jami'i da bai bayyan sunarsa ba ya ce an ɗauke mutanen wadanda suka hada da mutun ɗaya daga Togo da wani daga Madagascar, yayin da suke barci.

Wata sanarwar hadin gwiwa da kamfanonin Areva da Vinci suka fitar, sunce duk waɗanda aka kama ma'aikatan kamfanonin ne, kuma a ciki har da wani ma'aikaci da matarsa.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Umaru Aliyu