Garkuwa a matatar Gaz ta In Amenas | Labarai | DW | 18.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Garkuwa a matatar Gaz ta In Amenas

Dakarun gwamnatin Aljeriya na ci gaba da bata kashi da mutanen da suka yi garkuwa da ma'aikatan wata matatar iskan gaz

Har yanzu ana samun labarai masu cin karo da juna, game da garkuwa da wasu masu kaifin kishin addinin Islama suka yi a wani kamfanin haƙar iskan Gaz na ƙasar Aljeriya.

Gwamnatocin ƙasashen Turai da Amurika, wanda harin ya rutsa da mutanensu, sun yi Allah wadai ga matakin gaba gaɗe da hukumomin Aljers suka ɗauka, domin yin belin mutanen.

A ɗaya hannun, gwamnatocin sun koka da ƙarancin baiyani game da wannan ta'asa, saboda haka ne ma hukumomin Japan su ka gayyaci jikadan Aljeriya a birninTokiyo domin ya amsa tambayoyi.

A yayin da ya ke baiyani tare da DW, kakakin ministan harkokin wajen Nowe, Kjatil Elsebutangen, ya koka da ƙarancin baiyanin:

Har mu na cikin jiran samun labarai, ba mu da cikkakar masaniya game da halin da ake ciki saidai kawai jita-jita ta yi yawa.A yanzu an ce akwai bakwai daga cikin 'yan ƙasar Nowe da suka rasa rayuka, to amma kamar yadda na ce har yanzu bau tabbas.

Ya zuwa wannan lokaci babu wanda zai iya haƙiƙance yawan mutanen da suka mutu, ko wanda su ka ji raunuka.Saidai wani mai magana da yawun ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin, ya tabbatar da mutuwar mutane kimanin 50.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita:Halima Balaraba Abbas