1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO na son kasashe su kara sanya ido kan Covid-19

April 20, 2020

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta gargadi kasashen duniya a kan lallai su ci gaba da daukar matakan magance cutar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3b9k5
Schweiz Genf | WHO | Coronavirus | Tedros Adhanom Ghebreyesus, Generaldirektor
Hoto: picture-alliance/Photoshot

Wannan gargadi na zuwa ne a yayin da a wannan Litinin wasu kasashen duniya musamman a nahiyar Turai ke shirin fara sassauta dokokin da suka sanya na rage yaduwar cutar.


Shugaban hukumar  Tedros Adhanom Ghebreyesus  ya shaida wa wani taron ministocin kiwon lafiya na kasashe masu tattalin arzikin duniya na G20 cewa duk da cewa akwai karfafa gwiwa aji cewa kasashe za su fara komawa kamar yadda ake rayuwa a baya, amma a sanya ido sosai domin wannan ba ya nufin cewa ba za a samu karin barkewar cutar a kasashen ba, yana mai gargadin kasashen da su kasance a cikin shirin ko-ta-kwana.

Kasashen da ke da burin fara sassauta dokar kulle daga Litinin din nan sun hada da Jamus da Czech Republic da Faransa da Norway da Albania da kuma Poland.