Gargadin likitoci kan larurar warin baki | Zamantakewa | DW | 03.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gargadin likitoci kan larurar warin baki

A Najeriya a sakamakon karuwar masu fama da larurar warin baki, likitocin hakora da sauran kwararru a bangaren kiwon lafiya sun fara wayar da kan al'umma a kan hanyoyin rigakafin kauce wa kamuwa da wannan matsala.

A Najeriya a sakamakon karuwar masu fama da larurar warin baki, likitocin hakora da sauran kwararru a bangaren kiwon lafiya sun fara wayar da kan al'umma a kan hanyoyin rigakafin kauce wa kamuwa da wannan matsala da wasu lokuttan ke haifar da tsangwama ga masu fama da ita.

A sakamakon koke-koken da jama'a suka yawaita da a mu'amalarsu da masu fama da larurar warin baki ce ta sanya wasu likitocin hakora da sauran kwararru a bangaren kiwon lafiya da masana halittar dan Adam suka fara tashi tsaye wajan tabbatar da ganin cewa sun fargar da al'umman birane da karkara a kan mahimancin binciken lafiyar hakoka bayan kowadanne watanni shida ,domin dai rage matsalolin da ke janyo karuwar jama’a masu fama da larurar warin baki wanda a wasu lokutta ke sanya al'ummar gari kaurace wa duk wani da ke fama da wannan larura.

Malama Amina Ibrahim Marafa wata kwararriyar likitan Hakori ce a Kaduna ta bayyana cewa larurar warin baki babbar matsala ce da ya kamata al'umma su maida hankali a kai wajan kaucewa kamuwa da ita, tare ma da bayar da wasu shawarwari ta yadda mutun da kansa zai iya tantance ko yana fama da wanann larura ta warin baki ko kuma ba shi da ita. Likitan ta bayyana cewa so tari wannan matsala ta warin baki na lalata zaman aure da ke kaiwa a wasu lokuttan ga mutuwarsa baki daya sabili da yadda daya daga cikin ma'auratan ke kasa hakuri da larurar warin bakin abokin zaman nasa.

Likitar ta kara da cewa a likitocin hakora suna sha wahala wasu lokuta wajan wanke hakoran wasu mutanen da dandazon dauda ta mamaye su, domin sau tari masu ire-iren wadannan matsaloli idan ana wanke masu baki, ana samun zubar jini da yawa.

Dr Maryam Abdulrahman wata ita ma kwararriyar likitta a Najeriya,ta ce tun da farko abun da ya kamata al'umma ta sani shi ne, rashin kula da tsaftar baki ,shi ne musabbabin abun da ke janyo matsalolin da ke haifar da warin baki da kuma lalacewar hakora. Likitar ta ce daga cikin abubuwan da ke haifar da wannan matsala akwai rashin kwankwale sauran abinci da ke makalewa a hakori a lokacin cin abinci. Sannan ta ce wasu daga cikin matakan da ke taimakawa wajen kare mutun daga kamuwa da wanann larura ta warin baki, sune wanke baki kafin mutun ya shiga barcin dare da kuma bayan tashi daga barcin da safe.