Gargadin duniya game da zaben Gini-Bisau | Labarai | DW | 27.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gargadin duniya game da zaben Gini-Bisau

Majalisar Dinkin Duniya ta yi barazanar ladabtar da wadanda za su yi karar tsaye a harkokin zaben Gini-Bisau da za'a gudana a ranar 13 ga watan Afirilu mai zuwa.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci gwamnatin rikon kwarya ta Gini- Bisau da ta mutunta jadawalin zabe da ta fitar, tare da yin barazanar ladabtar da duk wani mahalukin da zai haifar da tafiyar hawainiya a kokarin da ake yi na mayar da kasar kan turbar demokaradiya. Su dai hukumomin Bisau sun tsayar da 13 ga watan Afirilu na wannan shekarar a matsayin ranar da za a gudanar da tagwayen zabuka na shugaban kasa da na 'yan majalisa bayan an dagesu so da dama.

Bisa ga tsarin farko dai, shekara guda bayan hambarar da gwamnatin Carlos Gomes Juniro a ranar 12 ga watan Afirlun 2012 ne ya kamata a gudanar da wadannan zabuka. Sai dai wasu matsaloli na siyasa da kuma babakeren sojoji sun haifar da tsaiko a fagen siyasar Gini-Bisau, tare da jefa tattalin arzikinta cikin wani mawuyacin hali.

Mambobin kwamitin sulhi na Majalisar Dinkin Duniya sun gargadi sojoji da kada su kuskura su yi shishshigi a harkokin zaben Gini-Bisau ko kuma su kin amincewa da sakamako. Gwamnatin wucin gadi da sojoji suka amince da ita ce ke jagorantar Gini- Bisau a halin yanzu. Wannan kasa da yammacin Afirka da ta samu 'yancin kanta daga Portugal shekaru 40 da suka gabata, ta yi kaurin suna a sigar amfani da tsinin bindiga wajen hambarar da gwamnati.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar