Gargadi game da shirin nukiliyar Koriya | Labarai | DW | 02.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gargadi game da shirin nukiliyar Koriya

Sakatere janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon ya ja kunnen koriya ta Arewa game da shirinta na farfado da cibiyarta ta nukiliya inda ya ce zai iya haddasa rikici a duniya.

Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon ya gargadi koriya ta Arewa game da aniyarta ta farfado da tashar nukiliyarta da ta daina aiki tun shekaru shidan da suka gabata. Ban ki-moon ya ce hukumomin Pyong Yong na neman zarta makadi da rawa, saboda hadarin da ke tattare ga yunkurin na su.

Ita dai Koriya ta Arewa ta ce ta dauki matakin farfado da murhunta na nukiliya domin samar da karin makamashin lantarki da al'umarta ke bukata. Sai dai kuma tana takun saka da takwarata ta kudu da kuma Amurka da ke mara mata baya, inda ta girke na'urorinta na kakkabo rokoki akan iyakokin kasashen biyu.

A shekara ta 2007 ne ita matalauciyar kasar ta Asiya ta amince ta dakatar da shirinta na nukiliya, bayan da kasashen duniya suka amince su ba ta tallafi. Sai dai kuma ta ki manyan jami'an hukumar makamashi ta duniya sun kai ziyarar gani da ido tasoshinta na nukiliya, inda maimakon haka ta janye daga tattaunawa da ta ke yi da kasashen China da Amurka da Japan da Rasha da kuma koriya ta kudu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh