1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garanbawul a ma'aikatar 'yan sandan Mexico

Yusuf BalaNovember 28, 2014

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da dauki ba dadi tsakaninin jami'an tsaro bayan mutuwar wasu dalibai 43 da suka bace, bincike ya gano kuma an kashesu an kone.

https://p.dw.com/p/1DvcK
Mexiko - Präsident Enrique Pena Nieto
Enrique Pena Nieto shugaban MexicoHoto: Getty Images/A. Estrella

Shugaban kasar Mexiko ya ce shirin zai samar da sauye-sauye a ma'aikatar 'yan sandan kananan hukumomi a kasar, saboda alakanta da ayyukan ta'addanci, a daidai lokacin da ake ci gaba da zargin 'yan sandan na hada kai da kungiyoyin 'yan ta'adda wajen aiwatar da ayyukansu.

Wannnan lamari kuwa na zuwa ne adaidai lokacin da ake ci gaba da dauki ba dadi da jami'an tsaro bayan gano mutuwar wasu dalibai 43 da suka bace.

Ana dai ci gaba da rasa rayuka na al'ummar kasar ta Mexico sa'oi ma kadan kafin bayyanar sanarwar shugaba Enrique Pena Nieto, lokacin da aka gano wasu gawarwakin mutane da aka yankasu a yankin Guerrero, da ke a kudancin kasar ta Mexico. Yankin dai da aka kai farmaki ga daliban a watan Satumba.

Pena Nieto ya bayyana cewa al'ummar kasar na ci gaba da daga murya cewa, sun gaji da ganin wannan salwantar rayuka, ta hanyar gudanar da zanga-zanga, abin da ke kara nunawa a fili irin alakar da 'yan sanda da harkokin da suka shafi cin hanci da rashawa.