Gano kasusuwa masu tsayin gaske a Niger | Zamantakewa | DW | 20.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gano kasusuwa masu tsayin gaske a Niger

Masana binciken kayyakin tarihin Misrawa sun gano wasu manyan kasusuwan gawarwakin da ake zaton na dan Adam ne da tsawonsunsu ya zarta mita shida.

Maitre Soule Garba Masanin wanda ke nazari a kan alakar Misrawa da Hausawa ya gano wadannan kasusuwa ne a wani gari mai suna Dankurhwa da ke da nisan kimanin kilomita biyu da dalar dutse a kauyen Danbaki na cikin jihar Damagaram ta jamhuriyar Nijar.

Tun da farko dai Soule Garba wanda kwararre ne a fannin ilimin binciken tarihin Misrawan musamman dangane da abun da ya shafi haruffan rubuce-rubucensu, ya yi nasarar warware ma'anar haruffan rubutun Misrawa cikin harshen Hausa, abin da kuma ya ba shi kwarin gwiwar cewa Misrawan da na zamanin fira'auna na magana a cikin harshen Hausa. Hakan kuma ya bashi damar karanto wasu labarai da ke kunshe a cikin littafan nasu da kuma abun mamakin da ke cikin kalmomin Hausa dama sunayen garuruwan duniyar Hausa a yau.

Maitre Sule Garba ta wanann haya ce ma dai ya yi nasarar gano dalar dutsen garin Danbaki a garin Tirminin jahar Zinder a yau sama da shekaru biyu.Dalar dutsen da ya bayyana ta a matsayin dalar dutse na farko da aka yi a duniya tun kafin ruwan dufana, da tuni ta gabaci gine-ginen pyramide din da ake gani a yau a kasar Masar. A ci gaban binciken neman tabbatar da sahihancin wannan labarin nasa na nuna kasar Hausa ita ce tushen duniya, Maitre Sule ya kuma gano wadannan manyan kasusuwan da tsawonsu ya wuce mizani a kauyen Dankurhwa.

Yanzu haka dai tarin kasusuwan irin wadannan dogwayen gawarwaki ne ke akwai barkatai a cikin kushewun kwarin garin na Dankurhwa a ko wane kewaye da kananan duwatsu, kuma wani dattijo dan kimanin shekaru dari da ke rayuwa a wanann kauye na ya ce kakanninsu ma anan su ka iske wadannan kasusuwa masu ban mamaki.

Mawallafi: Gazali Abdou daga Yamai
Edita:Yusuf Bala