1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin yaki da sauyin yanayi a manyan kasashe

Zulaiha Abubakar
November 29, 2019

'Yar fafutukar kare muhalli daga barazanar sauyin yanayi da ta yi suna a duniya Greta Thunberg ta sake fitowa cikin zanga-zangar birnin Lisbon na kasar Portugal don tilasta wa jagorori kan batun. 

https://p.dw.com/p/3Ty7W
Deutschland Klimademonstration "Fridays for Future" | Greta Thunberg und Luisa Neubauer
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Dubban al'umma a kasar Ostraliya da wasunsu a sassan kasashen Turai sun bi sahun wasu kungiyoyi wajen matsa wa shugabannin siyasa lamba don su gaggauta lalubo mafita game da matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa a lokacin taron Majalisar Dinkin Duniya da ake shirin farawa a birnin MAdrid na kasar Spain.

Wani jirgin ruwan da ke dauke da Thunberg din ya samu tsaiko a tekun Atlantic sakamakon iska mai karfi kamar yadda ta bayyana wa abokan huldar ta a shafukan ta na sada zumunta.

Zanga zangar sauyin yanayin a wannan Juma'ar na gudana ne a biranen da yawansu ya kai 2,200 tsakanin kasashe 153 a fadin duniya la'akari da kididdigar da kungiyoyin kare yanayi mai taken Fidays for Future suka fitar.