Gangamin adawa da tazarce a Kwango
August 23, 2016'Yan adawa da shugaban kasar Kwango sun gudanar da wani gangami a ranar Talatan nan bayan da suka kira wani yajin aiki na gama gari bisa bukatarsu ta ganin shugaban kasar ya sauka daga mukaminsa da zarar ya kammala wa'adin mulkinsa a watan Disamba mai zuwa.
'Yan sanda dai sun yi amafani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa gangamin daruruwan mutane a shedikwatar 'yan adawa mafi girma da ke lardin Limete a Kinsasha kamar yadda wadanda suka ga lamarin suka sheda wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Da safiyar Talatan nan dai a kwai karancin jama'a a titunan birnin Kinsasha sabanin yadda aka saba, wasu shaguna a rufe, wasu mutane na zaune a gidajensu. Sai dai a bangaren kamfanoni na hakar ma'aidanai da anan ne 'yan kasashen waje suka fi zuba jari harkoki na gudana. a