1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin adawa da gwamnati a Turkiyya

March 12, 2014

Dubun dubatan Turkawa sun fantsama kan tituna domin nuna adawa da gamnati, dangane da mutuwar wani yaro daga raunin da ya samu a zanga-zangar adawa a bara.

https://p.dw.com/p/1BOXJ
Berkin Elvan Begräbnis 12.03.2014 Istanbul
Hoto: Reuters

Dubun dubatan Turkawan da ke zaman makokin mutuwar wani yaro, sun hallara a tsakiyar birnin Istanbul, da ke zama cibiyar kasuwancin Turkiya, inda galibinsu ke yin kalaman batanci ga hukumomin kasar. Hakan dai na zuwa ne sakamakon mutuwar wani yaron da ya sami rauni yayin boren adawa da gwamnati a shekarar da ta gabata, wanda kuma aka yi jana'izarsa a wannan Larabar. 'Yan sandan kwantar da tarzona sun yi ta harba hayaki mai sa hawaye da kuma albarussan roba, akan masu zanga zangar da suka fantsama akan titunan biranen Turkiya daban daban, bayan samun labarin mutuwar Berkin Elvan a wannan Talatar, a wani abin da ke zama karin matsin lamba ga fira ministan kasar Recep Tayyip Erdogan, wanda ya samu kansa cikin badakalar cin hanci da rashawa, a dai dai lokacin da yake shirye shiryen tinkarar sabbin zabuka. Sai dai duk da jerin boren adawar da ya ke fuskanta, wasu manazarta na ganin cewar, Erdogan, na da damar sake yin nasara a zaben, da kuma shawo kan kalubalen da ya ke fuskanta.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal