Gangami a birnin Bangui kan rikicin addini | Labarai | DW | 28.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gangami a birnin Bangui kan rikicin addini

Al'amura na tafiyar hawainiya a Bangui sakamakon tashin hankali da ya barke a karshen Mako, wanda ya hallaka mutane da dama tare da sa jama'a yin ganganmi.

Daruruwan 'yan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun gudanar da gangami a kusa da fadar shugaban kasa a Bangui babban birni da nufin yin kira ga kasashen duniya da su dawo da doka da oda a kasar. Wannan dai ya biyo wani sabon rikicin addini da ya barke a Bangui a karshen mako inda mutane sama da 30 suka rasa rayukansu.

Duk da cewar firaministan Mahamat kamoun ya kafa dokar hana yawan dare, amma kuma wasu da ke dauke da bindigogi sun banka wa gidaje da dama wuta a dare jiya Lahadi zuwa yau Litinin.

Al'amura sun tsaya cik a Bangui babban birni inda shaguna suka kasance a rufe, yayin da babu dai motocin da ke zirga-zirga a manyan titunan birnin. Sai dai kuma sojojin kiyaye zaman lafiya suna sintiri domin kwantar da kurar rikicin da ka iya kunno kai.

Tun dai shekaru biyun da suka gabata ne dai rikicin kabilanci da na addini ya kunno kai sakamakon juyin mulki da 'yan tawayen Seleka suka yi.