Ganawar kantomar Ƙungiyar Taryyar Turai kan manufofin ƙetare da jami′an Majalisar Ɗinkin duniya a Gaza | Labarai | DW | 18.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar kantomar Ƙungiyar Taryyar Turai kan manufofin ƙetare da jami'an Majalisar Ɗinkin duniya a Gaza

A matsayin yanki na da ta ke yi ƙoƙrin domin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, kantomar Ƙungiyar Taraayar Turai kan manufofin ƙetare na kan ziyara a Gaza.

default

Catherine Ashton, kantomar Ƙungiyar Tarayyar Turai kan manufofin ƙetare.

Catherine Ashton, kantomar Ƙungiyar Tarayar Turai kan manufofin ƙetare ta na nan tana ganawa da jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya a zirin Gaza domin gano yadda ake amfani da kuɗaɗen taimako da Ƙungiyar Tarayyar Turai ke bai wa yankin da ke ƙarƙashin ikon ƙungiyar Hamas. Ashton tana kan wannan ziyara ne a matsayi yanki na rangadin yini biyar da ta ke yi a yankin Gabas ta Tsakiya inda tuni ta ya da zango a Masar, Siriya, Libanon, Jordan, Isra'ila da kuma Gaɓar yamma da Ƙogin Jordan. Sai dai kuma an fuskanci harin rokoki a kudancin Isra'ila yayin wannan ziyara tata, da yayi sanadiyar mutuwar wani ma'aikaci ɗan kasar Thailand. Ashton ba ta yi wata-wata ba ta yi Allah wadai da wannan hari. A gobe juma'a ne idan Allah ya kaimu jami'ar ta Ƙungiyar Tarayyar Turai za ta zarce zuwa birnin Moscow domin shiga taron rukunin nan na Quartet da zai shawarta hanyoyin komawa ga tafarkin samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falisɗinawa.

Mawallafiya Halima Abbas

Edita Ahmed Tijani Lawal