1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Jonathan da shugabannin Musulmi

October 15, 2013

Shugaban Najeriya ya yi wannan ganawar ce a bangaren bukin babban sallah, inda ya ce gwamantinsa bata da burin cin zarafi ga al'ummar Musulmi balle yanke kauna.

https://p.dw.com/p/1A08t
epa02694086 (FILE) A photograph dated 10 February 2011 shows Nigerian men walking in front of a banner of president Goodluck Jonathan at a Peoples Democratic Party (PDP) campaign rally in Kaduna north western Nigeria. Nigeria's president has been declared the winner of the oil-rich nation's election although there have been opposition riots in the north of the country. Election chairman Attahiru Jega announced results 18 April 2011 that showed President Goodluck Jonathan easily beat his nearest rival, former military ruler Muhammadu Buhari. EPA/GEORGE ESIRI
Hoto: picture-alliance/dpa

Ga dai rikicin Boko Haram din dake lafawa da sake tashi kamar dai gobarar da ta sha aradu sai ta yi kisa, sannan kuma ga sabon matakin gwamantin kasar na tattaunawa da nufin samar da makoma a kasar, abun kuma da tuni ya fara daukar fassarar da ta hada da yiwuwar rabewar kasar gida gida.

Ga kasar ta Najeriya da cikin kasa da wattani uku masu zuwa ke cika dari da hadewa amma kuma zuciyar al'ummarta ke rabe ya zuwa gida gida.

To sai dai kuma a wani taro na gaisuwar sallah tsakanin sa da shugabannin al'ummar musulmin kasar ta Najeriya dai, shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya ce, babban burin sa da ma daukacin jami'an da ke taka rawa a gwamantin sa dai na zaman hada kan Najeriya ya zuwa kasar da kowa ke iya alfaharin kanta, maimakon rabuwar kawunan da ma kila neman a raba tan da yanzu haka ke zaman salatin dake bakunan wasu yan kasar.

“A matsayin 'yantacciyar kasar da ke cin gashin kawunan mu dai bamu wuci shekaru 53 ba. Eh shekaru ne masu yawa ga dan adam na yanke hukunci. Amma ga kasa har yanzu mu kanana ne. Shi yasa muka dukufa domin iyakacin kokarinmu da ni da mataimakin shugaban kasa dama ragowar 'yan majalisar Ministoci na da kuma majalisun tarrayar mu, wajen ganin barin gadon Najeriya ga 'ya'yan mu na gobe da ke tasowa, Najeriyar da kowa zai zauna a cikin lafiya, Najeriyar da ko ina kaje zaka kira dan kasar dan uwanka. Kasar da in 'ya'yan mu sun girma za su yi alfahari da cewa su 'ya'yanta ne. Ba Nigeriyar da kila wani zai so kashe dan uwansa saboda kawai ba yarda dashi dan Najeriya bane”.

To sai dai kuma in har kalaman na shugaban kasar na shirin kara kwantar da hankula ga dimbi na musumnan kasar, ganawar tasa na zuwa ne a dai dai lokacin da al'amurra ke kara cabewa ga gwamantin dama al'ummar yankin arewa maso gabashin kasar in da yaki da ta'addancin kasar ya kasa ci balle kuma cinyewa.

Abun kuma da ya dauki hankalin massalatan idi da dama anan abuja dama ragowar sassan arewacin kasar dake kallon karatun da biyu, da kuma ke hadin addu'a da tsinuwar albarka ga manyan dillallan rikicin da ya hallaka dubban al'ummar yankin sannan kuma ya rusa daukacin harkoki na kasuwanci.

Ita ma dai kungiyar Amnesty mai faftuka ta kare hakkin bil'adama a birnin londin dai tace an ci zarafi an kuma musguna cikin cewar kungiyar ya kai ga gano gawar mutane kusan dubu guda da aka yiwa kisa irin na gila a gidan yari.

To sai dai kuma kwamitin da gwamantin kasar ta nada don tattunawa da yayan kungiyar Boko haram yace yai nasara a kokarin shawo kan rikicin a cewar Kabiru Tanimu Turaki dake zaman shugaban kwamitin da kuma ke shirin kammala aikinsa kowane lokaci daga yanzu.

Abun jira a gani dai na zaman mafita ga kasar da ke tsakanin kawo karshen aiyyuka na yan ta'adda da kuma kare makomar dubban al'ummar da fushin yakin ke tafiya da rayukansu cikin kasar.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Nuna karin labarai