Ganawar jami′an Amirka da Jamus | Labarai | DW | 18.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ganawar jami'an Amirka da Jamus

Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel ya bukaci taimakon kasar Amirka wajen ganin an warware takaddama tsakanin Jamus da kasar Turkiyya.

A wata ganawa da takwaransa na Amirka Rex Tillerson, manyan jami'an biyu sun tattauna batun kin amincewar da Turkiyya ta yi na 'yan majalisar Jamus su kai ziyara ga sojojin Jamus da ke Turkiyyar.

Kasar Turkiyya dai ta ce kin amincewar, martani ne ga mafakar da Jamus din ta baiwa sojojin Turkiyya, bayan yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Erdogan a bara.

Ministan harkokin wajen na Jamus dai ya ce yana da yakinin Amirka za ta yi amfani da tasirinta wajen kiran inganta dangataka tsakanin kasashe manbobin kungiyar tsaro ta NATO.