Gambiya za ta fara zartas da hukuncin kisa ga fursuna | Labarai | DW | 18.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gambiya za ta fara zartas da hukuncin kisa ga fursuna

Shugaban ƙasar Gambiya Yahya Jammeh ya yi gargaɗin cewar za su aiwatar da hukunci kisan nan gaba kaɗan

Shugaban ya ce za su aiwatar da hukuncin ga dukkanin fursunonin da ake tsare da su a gidajen yari waɗanda ke jiran a aiwatar da hukuncin kisan a kansu bayan kotu ta yanke musu shari'a.

A lokacin wani gangamin da ya yi tare da shugabannin addinai wanda gidan telbijan na ƙasar ya yaɗa,shugaba Jammeh ya ce za su yi haka ne saboda yawan aikata laifukan kisan kai da ake samu a ƙasar a cikin lokaci ƙanƙane. A shekarun 2012 hukuncin kisan ta hanyar bindigewa da gwamnatin Gambiyar ta aiwatar a kan wasu 'yan kaso galibi 'yan ƙasashen makoɓta na Afirka ya janyo martanin daga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin kare hakkin jama'a