Gambiya ta fita daga Commonwealth | Labarai | DW | 03.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gambiya ta fita daga Commonwealth

Gwamnatin ƙasar ta ba da sanarwar ficewa daga cikin ƙungiyar da ta ƙunshi ƙasashe rainon Ingila, shekaru 48 bayan da ta amince shiga cikin ƙungiyar mai mambobi 54.

A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta bayyana a gidan telebijan na ƙasar, ta ce Gambiya ta yanke shawarar ficewa daga cikin ƙungiyar ta Commonwealth sannan kuma ƙasar ba za ta ƙara shiga cikin irin wata ƙungiya makamanciyar haka ba, mai rajin ci gaba da yin mulkin mallaka.

Ko da shike gwamnatin ba ta ba da ƙarin haske ba a kan sanarwa, amma wani babban jami'in ma'aikatar harkokin waje na ƙasar ya ce lamarin ba ya rasa nasaba,da batun kwamitin da ƙungiyar ta Commonwealth ta buƙaci gwamnatin ta kafa shekarar bara. Domin bincika zargin take hakKin bil addama da cin hanci da ake zargin gwamnatin Yahya Jammeh da aikatawa. A shekarun 2002 shugaban na Gambiya wanda ya zo a kan iko bayan juyin mulki, ya yi kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin domin soke ƙaiyade wa'adin tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal