Ga jumulla mutune 301 ne da suka rasu a Turkiya | Labarai | DW | 17.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ga jumulla mutune 301 ne da suka rasu a Turkiya

Tsawon kwanaki biyar, masu aikin ceto a ma'aikatar hakar Mu'adanai dake Turkiya sun kai ga lalubo gawawaki 301, na wadanda suka rasu sakamakon hadarin.

Masu aikin ceton sun kawo karshen ayyukan binciken da suke a ma'aikatar hako da Mu'adanai ta Soma a kasar Turkiya, bayan da suka samo gawa ta karshe da ta kai ga adadin mutun 301 na wadanda suka mutu sakamakon rugujewar wannan ma'aikata ta kalkashin kasa.

Yau dai kwanaki biyar da afkuwar lamarin wanda ya tayar da zanga-zanga kusan a ko'ina cikin fadin kasar ta Turkiya, inda masu zanga-zangar ke neman Firaminista Recep Tayyip Erdogan, da ya yi murabus sabili da acewar su sakacin hukuma ce, ya kai ga mutuwar daruruwan mutanen wannan ma'aikata.

A jiya Juma'a dai sai da jamiyan tsaro na 'yan sanda suka tarwatsa wata zanga-zangar ta mutane fiye da dubu 10 a Soma inda hadarin ya faru, inda yan sandar sukayi amfani da hayaki mai sa kwalla da kuma fesa ruwa mai karfin gaske wajan tarwatsa masu zanga-zangar.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohamed Abubakar