G20 na son arziki ya wadata a duniya | Labarai | DW | 16.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

G20 na son arziki ya wadata a duniya

Shugabannin kungiyar kasashen da suka fi karfin masana'antu sun amince da daga darajar tattalin arzikin duniya da sama da kaso biyu kan nan da shekara ta 2018.

Shugabannin kasashen na G20 sun nunar da cewa hakan zai bunkasa tattalin arzikin duniya da ma samar da ayyukan yi ga mutane da dama. Sun kuma amince da daukar kwararan matakai a kan kamfanonin da ke kin biyan haraji da ma batun daukar matakai a kan dumamar yanayi.

A yayin taron da suka gudanar a birnin Brisbane na kasar Ostareliya, shugabannin na G20 sun amince da ba da goyon bayansu ga asusun inganta muhalli na Majalisar Dinkin Duniya wato "Green Climate Fund", da aka kirkiro domin tallafawa kasashe matalauta wajen shawo kan matsalar sauyin yanayi. Wannan dai na kunshe ne cikin takardar bayan taro da suka fitar bayan kammala taron da suka gudanar a birnin Brisbane na kasar Ostareliya.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe