Fuskokin masu shirya shirin Ji Ka Ƙaru | Learning by Ear | DW | 22.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Learning by Ear

Fuskokin masu shirya shirin Ji Ka Ƙaru

Shirin Ji ka karu sai daɗa bunƙasa yake yi! An samu ƙarin ƙwararru masu sha'awar shirin da suka haɗe da mu domin ƙara kyautata shirin don jin daɗin masu sauraro. Ga dai fuskokin sabbin masu taimaka wa shirin Ji Ka Ƙaru

Matasa 'yan wasan kwaikwayo a Rwanda

Matasa 'yan wasan kwaikwayo a Rwanda

Tun bayan da tashar Deutsche Welle ta fara gabatar da shirin Ji Ka Ƙaru a haɗin guiwa da Maikatar Harkokin Wajen Jamus a farkon shekara ta 2008, tawagar tsara shirin ke samun bunƙasa ba ƙaƙƙautawa. A yau an wayi gari tawagar ta ƙunshi ƙwararru ashirin daga Afirka da Jamus. A tsakaninsu akwai manejoji da editoci da masharhanta da malaman fassara da ƙwararrun fasahar aiwatarwa. Dukkansu suna aiki ne kafaɗa-da-kafaɗa domin cimma wata manufa ɗaya: domin su samar da nagartattun shirye-shirye da zasu ƙayatar da masu sauraro, musamman matasa a dukkan sassa na duniya.

DW Learning by Ear Autor Njoki Muhoho

Njoki Muhoho

Njoki Muhoho 'yar ƙasar Kenya dake ba da shawara akan fasahar gudanarwa ta daɗe tana sha'awar fasahar rubuce-rubuce, lamarin da ya zama sana'arta ta biyu a halin yanzu. Shahararriyar mawallafiya da waƙe-waƙen adabi kuma 'yar jarida mai shirya finafinai, a halin yanzu haka ita ce ke jagorantar tsara wata salsala ta dramar neman canji mai taken "Changes" a wata tashar telebijin ta gabacin Afirka, wadda kuma ake nunarwa a sama da ƙasashe 50 na nahiyar Afirka. "Tsafta da cutar gudawa" shi ne aikin da aka danƙa wa Njoki a karo na uku a shirin Ji Ka Ƙaru. Ita ce dai da rubuta salsalar shirye-shiryenmu akan "sana'a da ilimi" da kuma "Yanar gizo da sabuwar fasahar yaɗa labarai".

Learning by Ear Autor Chrispin Mwakideu

Chrispin Mwakideu

Chrispin Mwakideu daga ƙasar Kenya ƙwararren ɗan wasan 'yar tsana ne da wasan kwaikwayo da kuma tsare-tsaren drama. Yayi sama da shekaru 10 ana damawa da shi a shirin. "Wasan Kwaikwayo don Raya Ƙasa", inda yake amfani da 'yar tsana da wasanni na drama domin tinkarar matsaloli na zamantakewa da siyasa da tattalin arziƙin ƙasa. A gare shi, shirin Ji Ka Ƙaru tamkar wata sabuwar alƙibla ce ma faɗakarwa. "A matsayina na marubucin wasannin kwaikwayo, ba kawai ina ji kamar ni ma wani ɓangare ne na salsalar da nike rubutawa ba, in kuma koyan abubuwa da dama a tsakanin wannan lokaci", in ji shi. Chrispin da shi ne marubucin salsalar shirin Ji Ka Ƙaru akan tsoma bakin al'uma a al'amuran siyasa da zazzaɓin cizon sauro da kuma "Ƙwallon Ƙafa a Afirka-ba wasa ne kawai ba.

Romie Singh Journalistin in Südafrika

Romie Singh

Romie Singh a yanzu haka tana aiki ne a matsayin mai tsara shirye-shiryen ilimantarwa ta gidan rediyo da rubuce-rubucen litattafai da ba da horo a Johannesburg. Ta fara aiki ne a matsayin 'yar jarida ta rediyo kuma edita da gabatar da shirye-shirye a tashar Deutsche Welle dake Jamus. Ta koma da zama Afirka ta Kudu a 1998. A shekara ta 2008 an tuntuɓi Romie a shirin Ji Ka Ƙaru don ta tsara wata drama ta rediyo mai taken: "Mala'ikan dake tare da kowa", dake da nufin yaɗa rahotanni akan HIV da AIDS. Ita ce kuma ta rubuta salsalar shirin tsarin iyali. Shirinna na Ji Ka Ƙaru na baya-bayan nan drama ce akan tattaunawar addinai dake ɗauke da taken: "Gada akan Gori".

DW Learning by Ear Autor Ndiaye Ibrahima

Ndiaye Ibrahima

Ndiaye Ibrahim an haife shi ne a Senegal kana yana aiki a matsayin marubuci, mai rawa da kaɗe-kaɗe. Ya kasance fitaccen mai bada labari akan Afirka anan Jamus. Da irin basirar da ya ke da ita akan harkokin shirya kaɗe-kaɗe, raye-raye da nishanɗantarwa, ya kan samu nasarar jan hankulan masu kallon wasanninsa. Akan haka ne ma tsohon shugaban ƙasar Senegal Abdou Diouf, ya bashi lambar yabo akan al'adu.

Zainab Aziz

Zainab Aziz

Zainab Aziz Salim ta yi bankwana da ƙasarta ta asali Kenya shekaru huɗu da suka gabata, sai dai tayi farin cikin bayar da gudummowarta wajen cigaban Afirka,ta hanyar rubuta labari wa shirin ji ka ƙaru. 'Yar jarida ce wadda tayi aiki da gidan Radiyon Kenya da sashin Kiswahili a Deutsche Welle. Ta mayar da hankali ne kan yaƙi da cutar HIV da AIDS. Ita ce ta rubuta shiri akan rayuwar yara Mata.

LbE Autor Yaya Boudani Burkina Faso

Yaya Boudani

Yaya Boudani ya kasance ɗan jarida da gidan Radiyon Pulsar a Burkina Faso, tun bayan da ya shamu shadar karatun Digiri a jami'ar Ouagadougou.A yanzu haka shine ke kulawa da nazarin ilimin aikin jarida acan. Abun farin ciki ne aiki wa shirin ji ka ƙaru a gareshi.

Henry Fotso ɗan Jarida ne da ke aiki a hukumar yaɗa labarun Afirka (AIC) a Kamaru. Ya yi imanin cewar wasannin kwaikwayon Radiyo na Ji ka ƙaru, misali ne na rayuwara Matasan Afirka. A ganinsa Yara matasa za su ɗauki darussa da jerin shirye-shiryen, domin tsara rayuwarsu.

Hope Azeda ƙwararriya ce akan batutuwan nishaɗantarwa da yaɗa labarai. 'Yar asalin Rwanda, ta rubuta tare da aiwatar da wasannin kwaikwayo akan muhimman batutuwa da suka shafi rayuwa. Tana dauke da takardar shaidar Diploma a fannin waka, rawa da wasan kwaikwayo daga jami'ar Makerere. Ita ce ta rubuta easan kwaikwayon Ji ka ƙaru akan kiwon lafiya.

Justine Bitagoye ta fara aiki ne a matsayin 'yar jarida da mai gabatar da shiri na Talabijin a ƙasarta Burundi. Sai dai kuma sananniya ce a wasu sassan Afirka. Justine tana da shaidar Digiri na biyu daga jami'ar Makere dake Kampala. Wa shirin Ji ka ƙaru, ta yi rahotanni dangane da illolin mayar da Duniya bai ɗaya.

Alex Billy Gitta ya kasance matashin ɗan jarida daga Uganda. Idan baya rubuta labari wa shirin ji ka ƙaru, ya kan aike da labaru da ɗumi-ɗuminsu wa karamar tashar Radiyon 93.3 KFM da ke birnin Kampala. Ya samu horo ne a cibiyar nazarin aikin jarida da gidajen Radiyon BBC da Deutsche Welle.

Sam Tolulope Olukoya sanannen ɗan jaridan Talabijin da Rediyo ne a ƙasarsa Nigeria. Yana aike rahotanni ne daga tsakiyar birnin Lagos inda ake hada-hada, kuma ya samu lambobin yabo da dama, saboda irin rahotanninsa masu jan hankali. Wa shirin Ji ka ƙaru kuwa, Sam ya haɗu da wasu matasa ƙwararru da suka yi nasara a fannoni daban-daban na rayuwa.

DW.COM