Frank-Walter Steinmeier ya gana da Buhari | Labarai | DW | 10.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Frank-Walter Steinmeier ya gana da Buhari

Minsitan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya kai ziyarar aiki Najeriya, inda ya yaba da kokarinta na dakile ayyukan ta'addancin kuniyar Boko Haram a kasar.

A ganawarsa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Frank-Walter Steinmeier, ya yi wa shugaban fatan ci gaba da samun nasaran maido da martabar kasar a idanun duniya. Sai dai ministan ya kuma kalubalanci sauran shuwagabannin nahiyar Afirka da su kara kaimi wajen yakar ayyukan cin hanci da rashawa da zai baiwa kasar jamus kulla alaka mai karfi tsakanin ta da nahiyar Afirka.

Frank-Walter Steinmeier ya ce Afirka ba wai rawa kawai ta ke takawa ba, mu ma muna neman hanyar da za mu bi wajen kara kyautata alakarmu da nahiyar. Najeriya na matsayin uwa maba da mama a Afirka, ta na da albarkatun kasa da kuma arziki mai yawa, sai dai kalubalen da ta ke fuskanta na dakile ci gaba a kasar musamman ma kalubalen rashin tsaro.