1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Flynn: Mahawara kan amsa laifin yin karya

Zainab Mohammed Abubakar
December 2, 2017

Tsohon mai bai wa shugaba Donald Trump shawara kan harkokin tsaro Michael Flynn, ya amsa laifin yin karya dangane da sa bakin kasar Rasha cikin zaben shugaban kasa da ya gabata

https://p.dw.com/p/2oe50
USA Michael Flynn beim Briefing im Weißen Haus in Washington
Hoto: Reuters/C. Barria

Mai shekaru 58 da haihuwa kuma janar na soja mai ritayan, ya kasance jami'in gwamnati mafi  girman mukami, da ake zargi dangane yiwuwar hannun Rasha a zaben Amurkan na 2016.

Tsohon jami'in, ya bayar da bayanan karya ne ga hukumar binciken manyan laifukan Amurka ta FBI, a binciken da aka gudanar cikin watan Janairun wannan shekarar, dangane da tattaunawar da jakadan Rasha ya yi a karshen watan Disambar bara, mai alaka kai tsaye da zaben Amurkan.

Michael Flynn ya taka rawa lokacin yakin neman zaben shugaba Donald Trump, kuma fadar White House ta ce shi kadai ne wannan laifi ya shafa.