Fitaccen Jarumin Wasannin Kwaikwayon Hausa | Amsoshin takardunku | DW | 03.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Fitaccen Jarumin Wasannin Kwaikwayon Hausa

Shehu Hassan Kano, ya yi fice, da farin jini, wajen barkwanci, kuma ya fara ne daga wasannin 'Dabe', da ake kira 'skills drama' a turance.

Shehu Hassan Kano, fitaccen dan wasan kwaikwayon nan na Hausa, wanda ya yi fice, da farin jini, wajen barkwanci, ya fara ne daga wasannin 'Dabe', da ake kira 'skills drama' a turance, tun yana dalibin makarantar firamare. Shi, haifaffen unguwar Fagge ne, da ke cikin kwaryar jihar 'Kanon Dabo Timbin Giwa', wanda bayan karatun allo, ya zarce karatun boko, inda ya yada zango a Kwalejin ilimi da ke jihar Kano, wato..F.C.E Kano.

Shehu Hassan Kano ya taba koyarwa a makarantar firamare har tsahon shekara guda, kuma ya yi aiki da kamfanin Dantata. Kawo yanzu, shi ma'aikacin Karamar Hukuma ne, a nan Kano, a bangaren karbar kudaden shiga. Kuma yana aikin yana gudanar da sana'ar yin fim, wato wasannin kwaikwayo.

A cikin finafinan da ya fito a ciki, fim din 'In da So Da Kauna' shi ne ya kasance bakandamiya a gareshi, kuma jarimin da yafi burge shi, shi ne; Ibrahim Mandawari, wanda kuma abokinsa ne. Sai Hauwa Ali Dodo, a bangaren mata, da akafi sani da 'Biba Problem'.

Har ila yau, yana da burin daya, daga cikin 'ya'yansa, ya gaje shi, a wannan sana'a, ta wasannin kwaikwayo. Amma babban burinsa, shi ne, tsaftace harkokin fina-finen na Hausa, ta hanyar bude makarantar karo ilimi kan harkokin wasannin, da aiwatar da gyare-gyare kan abubuwan da suka dace a wasannin na Hausa, dan ciyar da al'adu gaba.