Firimiyan Benin ya tsallake rijiya da baya | Labarai | DW | 27.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firimiyan Benin ya tsallake rijiya da baya

Wani jirgin sama mai saukar ungulu dauke da Firaministan Benin Lionel Zinsou ya fado a daidai lokacin da yake kokarin sauka, a filin kwallon kafa na garin Djougou.

Lionel Zinsou

Lionel Zinsou

Zinsou ya je garin Djougou da ke a yankin Arewa maso yammacin kasar ta Benin domin halartar wasu bukukuwa na Ganni da ake gudanarwa a duk watan Disamba na ko wace shekara a wannan yanki. Sai dai kawo yanzu ba'a gano musabbabin wannan hadarin jirgin mai saukar ungulu ba. Amma tuni aka soma bincike a kan lamarin. Wata majiya ce ta fadar shugaban kasar ta Benin ta tabbatar da wannan labari

A watan Yunin da ya gabata ne Shugaban kasar Yayi Bony Yayi ya nada Lionel Zinsou wanda yake da takardar zama dan kasar Faransa a matsayin Firaminista, kuma jama'a da dama na masa kallon wani wanda ka iya maye gurbin shugaban kasar a karshen wa'adin mulkinsa.