1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Turkiya ya goyi da bayan ɗage hanin ɗaura ɗan kwali a jami´o´i

September 19, 2007
https://p.dw.com/p/BuAx

FM Turkiya Rejep Tayyip Erdogan ya ce yana son a dage haramcin sanya dan kwali ga mata a jami´o´in kasar baki daya. FM na Turkiya ya fadawa jaridar Financial Times cewa bai kamata a kayyade ´yancin samun ilimi mai zurfi ga mata saboda tufafi da suke sanyawa. Shi ma shugaban kasar ta Turkiya Abdullah Gül ya furta irin wadannan kalamai. A dai halin da ake ciki gwamnatin jam´iyar AKP mai ra´ayin mazan jiya ta na aikin fasalta sabon kundin tsarin mulkin kasar. To sai dai ba´a sani ba ko za´a tabo batun dage haramcin sanya dan kwalin a jami´o´in kasar. Hana daura dan kwali a ma´aikatun gwamnati da jami´o´i a Turkiya ya samo asali ne sakamakon wani juyin mulkin soji a shekara ta 1980.