Firaministan Tanzaniya ya ce shugaban yana lafiya | Labarai | DW | 13.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Tanzaniya ya ce shugaban yana lafiya

Firaministan Tanzaniya Kassim Majaliwa ya yi watsi da ikirarin 'yan adawa na kasar cewa shugaban kasar John Magafuli na fama da cutar coronavirus.

Firaminista Kassim Majaliwa na kasar Tanzaniya ya yi watsi da ikirarin 'yan adawa na kasar cewa Shugaba John Magafuli ya bace daga idon al'umma sakamakon kamuwa da cutar coronavirus tun kimanin makonni biyu da suka gabata.

Firaministan ya ce shugaban yana dukufa ne kan ayyukan da ke gabansa shi saka aka daini ganin a bayyan jama'a. Amma Firaminista Majaliwa bai bayyana takamammen inda shugaban kasra yake ba.

Shi dai Shugaba John Magufuli na Tanzabiya ya ayyana cewa kasar ta samu nasara kan annobar cutar coronavirus a shekarar da ta gabata, sai dai yanzu ana yada labaran cewa rashin ganin shugaban akwai yuwuwar ya kamu da wannan cuta ta coronavirus.