Firaministan kasar Ethiopiya ya yi marabus | Labarai | DW | 15.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan kasar Ethiopiya ya yi marabus

Hailemariam Desalegn ya mika takardar barin aiki bayan da masu kin jinin gwamnatin kasar suka shafe watanni suna gudanar da zanga- zanga.

Sanarwar ta kara da cewar firaministan ya bayyana cewar daga cikin dalilansa na murabus akwai irin rigingimun kasar da ya yi bakin kokari wajen magancewa amma al'amarin ya ci tura, a don haka ya yanke sharawar sauka daga mulkin kasar don ya zama daga cikin masu nema wa  kasar mafita. A kwanakin baya ne dai gwamnatin kasar ta sako daruruwan irsinonin siyasar kasar da su ka jima a garkame a gidajen yarin.