Firaministan Indiya zai kai ziyara zuwa Turai | Labarai | DW | 08.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Indiya zai kai ziyara zuwa Turai

Firaministan kasar Indiya Narendra Modi zai kai ziyara zuwa kasashen Turai da ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki, domin neman zuba jari a kasarsa.

A ranar Alhamis Firaminista Modi zai kai ziyara kasar Faransa kafin daga bisani ya isa kasar Jamus. Modi ya kasance karkashin bakin littafin kasashen Turai na tsawon lokaci, bayan tashin hankalin da ya faru a Jihar Gujurat lokacin da yake rike da madafun ikon jihar a shekara ta 2002. Ana sa ran ziyarar za ta karfafa hulda tsakanin kasashen da kuma Indiya.

Firaminista Narendra Modi zai kammala ziyarar da kasar Kanada. Gwamnatin kasar ta Indiya ta dauki matakin kara taimakon manoma domin samun karin amfanin gona da rage mawuyacin halin da suke ciki.