1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu zanga-zanga 86 suka mutu a Habasha

Suleiman Babayo AH
November 3, 2019

Firaministan Habasha ya ce mutanen da suka mutu sakamakon zanga-zanga sun kai 86 cikin watan jiya.

https://p.dw.com/p/3SPG0
Äthiopien Addis Abeba Anhänger vor dem Haus des Oppositionsführers Jawar Mohammed
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Ayene

Firaminista Abiy Ahmed na kasar Habasha ya bayyana a wannan Lahadi cewa mutanen da suka mutu sakamakon zanga-zangar watan jiya sun kai 86 sannan ya bukaci 'yan kasar su nuna tirjiya ga masu barazana bisa ci-gaba da ake samu a kasar. Firaministan ya fadi haka yayin taro manema labarai da kofofin yada labaran gwamnati. An samu tashin hankali lokacin da wani fitaccen dan gwagwarmaya Jawar Mohammed ya yi zargin jami'an 'yan sanda sun kewaye gidansa da ke birnin Addis Ababa fadar gwamnatin kasar kana sun yi yunkurin janye masa jami'an tsaro. Gwamnatin ta Habasha ta ce tashin hankali ya shafi daukacin bangarorin al'ummomin kasar.