1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Finland ta jaddada kudirinta na shiga NATO

January 24, 2023

Ministan harkokin wajen Finland Pekka Haavisto ya ce ba gudu ba ja da baya a kudirin kasarsa na shiga kungiyar kawancen tsaro ta NATO

https://p.dw.com/p/4MeTl
Deutschland | NATO Außenministertreffen in Berlin | Pekka Haavisto
Hoto: /AP Photo/picture alliance

Kasar Finland ta jaddada kudirinta na shiga kungiyar kawancen tsaro ta NATO ko da ko ba da sahalewar kasar Turkiyya ba.

A cewar ministan harkokin waje na Finland Pekka Haavisto yayin hira da wani gidan talabijin na kasar, kasarsa ta dauki wannan kudiri ne bayan lura da jan kafa da takwararta kasar Sweden ke yi wajen cimma burinsu na shiga kugiyar kawancen tsaron.

To sai dai a daidai lokacin da Finland ta dauki wannan kudiri Turkiya da ke da karfin fada a ji a kawancen kungiyar ta NATO ta dage wata ganawa da ya kamata ta yi da Finland da Sweeden a farkon watan Fabrairu kan shirin shigar kasashen biyu kungiyar ta NATO.