1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: FBI ta fitar da kundin bincike

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 12, 2021

Hukumar Leken Asirin Amirka FBI ta fitar da kundin farko da ke da alaka da binciken da ta yi, kan harin da aka kai a kasar a ranar 11 ga watan Satumbar 2001.

https://p.dw.com/p/40DTV
USA | Terroranschlag am 11. September 2001
Cibiyar Kasuwanci ta Duniya da ke New York, na daga cikin inda aka kai harinHoto: NTV/epa/dpa/picture-alliance

Hukumar dai ta bi umurnin da shugaban Amirkan Joe Biden ne wajen fitar da kundin, kamar yadda iyalan wadanda harin ya rutsa da su suka bukata daga Biden din. Cikin kundin mai shafuka 16, an bankado yadda wadanda suka yi fashin jiragen fasinjan hudu suka rinka musayar bayanai da jami'an kasar Saudiyya. Sai dai har kawo yanzu, babu tabbacin ko Riyadh na da hannu a harin da ya halaka mutane 3,000.