1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban gwamnatin Libiya na ziyara a kasashen Turai

Abdoulaye Mamane Amadou
May 7, 2019

Shugaban gwamnatin hadin kan kasa na Libiya na wata ziyarar aiki kasashen Turai inda ya ke ci gaba da ganawa da hukumomin wasu kasashen, a daidai lokacin da batun tsaro da rashin kwanciyar hankali ke ta'azzara a Libiya.

https://p.dw.com/p/3I58x
Berlin Merkel und Libyscher Ministerpräsident Fajis al-Sarradsch
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Gambarini

Firaministan Libiya Fayez al-Sarraj ya yi wata ganawa a yau Talata da Giuseppe Conte shugaban gwamnatin Italiya, a yayin da a share daya babban abokin hammyar gwamnatin hadin kan kasar wato Khalifa Haftar ke ci gaba da kira ga dakarun da ke masa biyayya da su kara matsa kaimi a yunkurinsa na karbe iko ga gwamnatin birnin Tripoli.

Rahotanni sun ce ba wani sabon mataki da ya fito a bakunan shugabannin biyu,  bayan sun shafe dogon lokaci suna tattauanawa, sai dai an ambato Firaministan Italiya Giuseppe Conte na cewar matakin sojan da bangarorin kasar da ke rikici ke ci gaba da dauka ba zai haifar wa kasar da mai ido ba.

Bayan kasar Italiya al-Sarraj zai kuma gana wa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a Barlin a yau Talata kan daga baya ya wuce zuwa birnin Paris a gobe Laraba don yin wata tattauanawa da shugaban kasar Emanuel Macron.