Fatan warware rikicin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 20.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fatan warware rikicin nukiliyar Iran

Bayan tsawon shekaru na takaddama, a yanzu duniya na fatan ganin an warware rikicin nukiliyar Iran yayin sabuwar tattaunawa a birnin Geneva.

Iran da kasashen da ke da karfin fada a ji a duniya za su sake komawa ga tattauna batun nukiliyarta a birnin Geneva - a wannan Larabar, a kokarin da suke yi na cimma maslaha dangane da takaddama bisa shirin nukiliyar kasar ta Iran, da kuma shawo kan dari-darin da masu tsattsauran ra'ayi a Isra'ila da Amirka da kuma Iran ke da shi. Shugaban Amirka Barak Obama ya gana da jiga-jigai a majalisar dattijan kasar domin shawo kansu game da kaucewa sanyawa Iran karin takunkumi, wanda ka iya jefa tattaunawar diflomasiyyar cikin matsala, kana da sanya Iran cikin yanayin da za ta fadada shirin nukiiliyarta bayan dakatarwar da ta yi na wani dan lokaci. Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif, ya aike da sako ta shafin yanar gizo na You Tube gabannin taron, inda ya fadi a birnin Roma na kasar Italiya cewar, akwai yiwuwar cimma nasara. Sai dai kuma shugaba Obama na Amirka ya shaidawa wata mujallar Amirka cewar, ba shi cikakkiyar masaniyar ko za a iya cimma yarjejeniya, ko dai a makonnan ko kuma a mako mai zuwa ne.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu