1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fatan warware rikicin Mali ya dakushe

December 14, 2012

Matakin da sojojin Mali suka ɗauka na korar firaminista Cheikh Modibo Diarra na zaman mayar da hannu agogo baya a ƙoƙarin samun mafita ga rikicin ƙasar.

https://p.dw.com/p/172qf
Hoto: AFP/Getty Images

Jaridun na Jamus a wannan mako sun fi mayar da hankali ne a kann kasar Mali. A babban labarinta jaridar die Tageszeitung ta fara ne da cewa bayan sojoji sun tumbuke firaministan rikon kwarya, an maye gurbinsa da wani jami'i da ba a san shi ba sosai a bainar jama'a wato Diango Cissoko a matsayin sabon firaminista ga wata kasa da ta durƙushe.

„Cissoko mai shekaru 61, yayi aiki a karkashin gwamnatoci da dama a Mali. Kafin shekarar 2011 shi ne sakatare janar ga tsohon shugaban kasa Amadou Toure. Yanzu an dora wa Cissoko mai digirin digirgir a fannin shari'a, nauyin jagorantar kasar daga rikice rikicen da take fama da su. Da farko mazauna Bamako babban birnin kasar sun fusata da matakin da kaptain Amadou Sanogo ya dauka na fatattakar firaminista, amma daga bisani an fara fatan cewa watakila halin da ake ciki ka iya sauyawa, kasancewa jama'a ta fara dawowa daga rakiyar tsohon firaminista Cheick Modibo Diarra, domin ya kwashe lokaci mai tsawo ba ya cikin kasar, yana jiyya a kasar Faransa. Kana kuma bai mayar da hankali ga ci gaban Mali ba.“

Rikicin Mali ya dauki sabon salo

Rashin tabbas a Mali, inji jaridar Berliner Zeitung sannan sai ta ci gaba da cewa.

Amadou Sanogo
Amadou SanogoHoto: picture-alliance/dpa

„Mali ɗaya daga cikin kasashe matalauta a Afirka, ta ƙara tsunduma cikin rikici. Bayan kashi biyu cikin uku na kasar ya fita karkashin ikon sojoji da gwamnati, yanzu wani rikicin siyasa ne ya kunno kai, da zai kara dagula kokarin sake kwace yankin arewacin kasar daga hannun masu kishin Islama. Wannan aiki na bukatar kwanciyar hankali da daidaituwar al'amura a kudancin kasar.“

Tsbatataccen zabe a Ghana

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung tsokaci ta yi ga zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasar Ghana a makon da ya gabata. Ta ce:

Wiederwahl John Mahama in Ghana
Hoto: Reuters

„Jarrabawa ga kasar Ghana, 'yan adawa sun zargi shugaba Mahama da magudin zabe. Jaridar ta ce tun a lokacin yakin neman zabe aka fahimci cewa zaben na wannan karon zai dauki sabon salo inda tattalin arziki ya mamaye yakin neman zaben. Tun a shekarar 2010 Ghana ta fara hako man fetir, kasar na samun bunkasa. Yawan wadanda suka kada kuri'unsu ya kai kashi 80 cikin 100. Duk da cewa a wasu wurare an fuskanci matsalolin injunan tantance masu zabe, dalilin da ya sa aka tsawaita lokacin zaben a wasu mazabun, amma kasancewa wannan shi ne karon farko da kasar ta yi amfani da na'urar komfuta a zabe, ba abin mamaki ba ne fuskantar irin wanan matsala. Zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana yayin da tawagogin sa ido a zabe suka ce an yi zabe mai tsabta. Duk da cewa jam'iyar adawa ta nuna aniyar kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotu, amma jaridar ta ce hakan ba zai zama wata barazana ga kasar ta Ghana ba wadda ta yi fice wajen shirya sahihin zabe kuma take zama abar koyi ga kasashen Afirka.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh