Fatan tsagaita wuta a Sudan ta Kudu na durƙushewa | Labarai | DW | 13.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fatan tsagaita wuta a Sudan ta Kudu na durƙushewa

Al'ummomin ƙasa da ƙasa na kira ga shugabanin Sudan ta Kudu da su tabbatar da ɗorewar yarjejeniyar tsagaita wuta dan kawo ƙarshen rikicin ƙasar

Masu shiga tsakani, waɗanda suka jagoranci yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan ta Kudu, sun yi kira ga ɓangarorin da ke yaki da juna da su mutunta yarjejeniyar, ganin cewar babu alamun dakatar da zud da jinin da ke afkuwa duk da alƙawuran da suka yi a kan takarda. Faɗa za kaure tun ranar lahadi, wuni guda bayan da shugaba Salva Kiir da jagorar 'yan tawaye Riek Machar suka ƙulla yarjejeniyar da ta rushe, wanda ke zaman karo na biyu a tsukin watanni biyar.

Ɓangarorin biyu dai suna zargin juna da kai hari, kuma dakarun sojin ƙasar sun rawaito cewa 'yan tawaye sun kai hari sansaninsu da ke Dolieb, wanda ke kudu da garin Malakal wanda yaki ya cinye. Yarjejeniyar da suka rattaɓawa hannu a makon da ya gabata a Adis Ababa, ta yi mafari ne sakamakon matsin lambar da al'ummomin ƙasa da ƙasa suka ɗauki makonni suna yi, da ma sauran matakan diplomasiyyar da aka ɗauka.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Abdourahamane Hassane