Fata na karin albashin ma′aikata a Najeriya | Siyasa | DW | 27.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fata na karin albashin ma'aikata a Najeriya

A wani abun da ke zaman kama hanyar kaiwa ya zuwa darawa a banagren ma'aikatan Tarayyar Najeriya gwamnatin kasar ta kaddamar da sabon kwamitin tsara albashi.

Tun bayan karin farashin man fetur da gwamnatin kasar ta aiwatar a watan Mayu bara ne dai mahukuntan na Abuja suka dauki alkawarin karin albashin a cikin neman hanyar saukaka tsanani na rayuwar ma'aikata a Tarayyar Najeriyar.

To sai dai kuma sai da ranar Litinin ne Abujar ta kama hanyar cika alkawarinta tare da kafa wani kwamiti na mutane 30 da ya kunshi 'yan kwadago da gwamnoni da shugabannin kungiyoyin daukar ma'aikata da wakilai na gwamnatin tarrayar da nufin tantance ko nawa ne ya kamaci kasar ta biya da sunan mafi karancin albashin ma'aikata na gwamnatoci da ma kamfuna a Tarrayar Najeriyar.

Kafin yanzun dai kasar na biyan Naira 18,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikatan kasar, adadin kuma da ake yiwa kallo mafi karanci a tsakanin daukacin kasashen Yammacin Afirka a yanzu.

1. Mai in Nigeria (DW)

'Yan kwadago sun dade da kukan albashi

To sai dai kuma a fadar Boboi Bala Kaigama da ke zaman shugaban kungiyar manyan ma'aikatan kasar ta TUC, ma'aikata cikin kasar a halin yanzu dai na da bukatar Naira 56,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Kari a bisa tsada ta rayuwa ko kuma kokari na babakeren ma'aikata dai gashi ma Ayuba Wabba da ke jagorantar babbar kungiyar kodagon kasar ta NLC dai sabon matakin na zaman babba na cigaba a bisa alkawarin kyautata rayuwar 'yan aikin da suke ji a jiki.

To sai dai kuma a fadar Abubakar Atiku Bagudu da ke zaman gwamna ga jihar Kebbi daya kuma a cikin 'yan kwamitin albashin da ya ce jihohin kasar ba su da haufin karin albashin.

Sauti da bidiyo akan labarin