Fashewar wasu abubuwa a arewacin birnin London | Labarai | DW | 11.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fashewar wasu abubuwa a arewacin birnin London

Mutane 36 suka ji rauni amma daukaci ba rauni mai tsanani ba sakamakon fashewar wasu abubuwa da aka ce hadari ne a wani wurin ajiye mai dake kusa da birnin London. ´Yan sanda sun ce 4 daga cikin su sun samu munanan raunuka, to amma Howard Borket-Jones, daraktan asibitin West Hertfordshire ya ce mutum biyu kadai ne raunin su yayi tsanani kuma za´a ci-gaba da yi musu magani a asibiti. ´Yan sanda sun ce hadari ne ya haddasa fashewar abubuwan, to amma duk da haka sun ce za´a gudanar da bincike kafin a iya tabbatar da hakan.