Fashewar bama-bamai a Boston ta girgiza Amirka | Siyasa | DW | 16.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fashewar bama-bamai a Boston ta girgiza Amirka

Amirkawa sun shiga halin kibita bayan fashewar wasu tagwayen bama-bamai a birnin Boston a daidai filin da ake shirya wata gagaramar gasar tseren kafa.

Karan fashewar bam.

Daya kenan daga cikin bam din da ta fashe a birnin Boston a yammacin jiya a daidai lokacin da jama'a ta taru dankam ,ta na kallon masu gasar tseren kafa ta birnin.Wannan hari ya zuwa yanzu, ya haddasa asara rayuka uku da kuma jikata mutane da dama.

Tun bayan hare-haren 11 ga watan Satumba na shekara 2001, wannan shine karon farko da Amirka ta taba fuskantar irin wannan yanayi.

Gasar ta tseren kafa dake wakanan a birnin Boston, itace mafi tasiti a Amirka, wadda ke samun mahalarta daga ko ina cikin duniya.

Harisson Maina wani dan jarida ne dan asulin kasar Kenya wanda kuma shi ganau ne ba jiyau ba, ya ce saura kiris harin ya rutsa da wasu 'yan tsere daga Kenya da Ethiopiya:

"A lokacin da bam din ta fashe, akwai mutanen Kenya da na Ethiopiya da dama, wanda suka zo su kara karfin gwiwa ga masu tseren daga su ka zo daga wannan kasashen.Duk sun ketara rijiya da baya, domin bama-baman sun tashi jim kadan bayan gusawara su daga wurin"

A yayin da ya gabatar da jawabi ta kafar sadarwa, shugaba Barack Obama na Amirka ya ce gwamnatinsa za ta yi iya kokari ,domin gano masu alhakin wannan aika-aika:

"Kawo yanzu ba mu san wanda ya kai harin, kuma ba mu san dalili ba, ba za mu yi azarbabi ba,amma babu shakka za mu bankado ko suwanene kuma za su baiyana dalilin kai harin kafin su fuskanci shari'a."

Tun dai lokacin abkuwar harin,jami'an tsaron Amurika suka tsaurara matakan tsaro, ba wai kadai a Boston ba, har ma da wasu manyan biranen kasar da suka hada da Washington da New -York da kuma manyan filayen saukar jiragen saman kasar.

Hukumomin tsaro a Boston, sun yi kira ga al'uma su kwantar da hankula, kuma su takaita zirga-zirga kamar yadda Ed Davis, shugaban rundunar 'yan sandar Boston ya baiyana:

"A yanzu mu na kira ga jama'a kowa ya zauna gida wanda kuma ke cikin hotel-hotel dake kusa da wurin,su zauna dakunansu".

Daga sassa daban daban na duniya na ci gaba da yin Allah wadai da wannan hare-hare, wanda har ya zuwa wannan lokaci, babu wanda ya dauki alhakin shirya su.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin