Fasahar kwada zuciya | Himma dai Matasa | DW | 08.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Fasahar kwada zuciya

Wani matasa a kasar Kamaru ya kirkiro wata na'ura awun zuciya.

Mafi yawancin Al,ummar kasashen Afrika ta yamma ba su da kwararru a kan abin da ya shafi aikin zuciya, hakan ne ya sa, duk lokacin da aka samu kwararre kan hakan kan kasance da matikar tsada. A dalilin haka wani dalibi a kasar Kamaru ya yi tunanin kirkiro wata na'ura wadda ake kira Cardiopad.

Tin sanyin safiya cibiyar kula da harkokin lafiya ta Jami'ar Yawunde da ke kasar ta Kamaru ta cika makil da dalibai maza da mata da nufin ai masu awun zuciya da wannan na'ura da dalibin ya kirkiro. Abdouramane Gandai wani dalibi ne ya ce labarinn wannan na'ura a kafar Television ya gani.

A dalilin yawan hawan jini a kasar Kamaru kusan mutane 17,000 ke mutuwa duk shekara saboda awun cutar abu ne mai matikar tsada saboda ana kashe kusan Euro 30 wajen bunciken larurar zuciya, haka ne ya sa kowace shekara ana samun karuwar masu rasa ransu a kasar.

Arthur Zang shi ne dalibin daya kirkiro da wannan na'ura kuma yana aiki ne a kan wata kwamfutar hannu tsawan shekaru bakwai ya bayyana irin yadda ya bi ya kirkiro na'urar dama dalilan kirkirota:

Ya ce "Ni dalibi ne matashi kuma ina koyan aiki a wani asibiti a Yawunde na kasar Kamaru ta haka ne na gane cewa akwai karancin likitocin zuciya a cikin mutane milliyan 19 na kasar Kamaru ba a samun likitocin zuciya 40 shi ya sa nayi sha'awar samar da mafita dan haka da farko sai na yi wata manhaja da kuma kara ingantata ta haka ne na kirkiri na'urar a shekara ta 2011 kuma nike kiranta Cardiopad"

Bankuna Kamaru sun yi tirjiya wajen taimakon Zang da rancen kudi dan gudanar da aiki haka ne ya sa ya nemi kafafen sada zumunta na zamani na a tallafa masa kuma kiransa ya samu karbuwa inda kamfanin manhajar kasar Amirka ya ba shi 26,000 Euro wadanda yai amfani da su a Kamfaninsa ya yi na'urori 20 wadanda kuma ake amfani da su a asibitoci a halin yanzu.

Ita dai wanna na'ura da Zang ya kirkira tanad a matukar saukin sarrafawa, ana saka ta a jikin mara lafiya wata na'ura ta haska bayanai mara waya a kirjin mara lafiya inda shi likita zai ga abin da ke damun zuciyar.