1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jack Warner ya ce yana da shaidar rufa-rufa a hukumar FIFA

Yusuf BalaJune 4, 2015

Warner tshohon mataimakin shugaban hukumar FIFA ya ce akwai wasu takardu da yake da su da suka jibinci batun harkokin da suka shafi kudi a hukumar ta FIFA da zai bayyana.

https://p.dw.com/p/1FbbL
Jack Warner
Jack Warner tshohon mataimakin shugaban FIFAHoto: Getty Images/AFP/L. Acosta

Tsohon mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Jack Warner da ke a tsakiyar batun badakalar cin hanci da rashawa a hukumar ya yi alkawarin cewa zai fadawa masu bincike duk abin da ya sani da ya shafi batun cin hanci da rashawa a cikin hukumar wasannin.

A wani jawabi da yayi ta kafar yada labaran tsibiran Trinidad da Tobago a yammacin jiya Laraba, Jack Warner ya ce duk da cewa yana da fargaba kan makomar rayuwarsa amma zai bayyana duk abinda ya ke da masaniya akai.

Ya ce tuni ya bawa lauyoyinsa umarni su tattauna da jami'an tsaro a cikin kasarsa ta haihuwa da ma wajenta.

Batun bashi kudi kuwa da ake zargin Afirka ta Kudu da yi bai ma taso ba:

Ya ce "Ba gaskiya bane cewa kasar Afrika ta Kudu ta bani wani kudi wai Dala miliyan goma a matasyin cin hanci , basu bani cin hanci ba"

Warner ya ce akwai wasu takardu da yake dasu da suka jibinci batun harkokin da suka shafi kudi a hukumar ta FIFA da tuni mahukuntan Amirka suka gudanar da bincike a kansu , sannan yana da wasu takardun da suke da alaka tsakanin FIFA da zaben gwamnatin Trinidad da Tobago a shekarar 2010. Ya kara da cewa lokaci ya yi na a bayyana komai ba sauran boye-boye.