1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farmakin karshe kan Boko Haram a Najeriya

Al-Amin Suleiman Muhammad | Abdul-raheem Hassan
May 15, 2018

Nan da Satumba rundunar soji ta yi ikirari kakkabe Boko Haram, domin ba wa mazauna tafkin Chadi damar cigaba da rayuwa a yankunansu.

https://p.dw.com/p/2xm0w
Symbolbild Nigeria Armee
Hoto: picture alliance/AP Photo/Gambrell

Yayin wani taro na musamman a birnin Maiduguri na jihar Borno, rundunar sojojin Najeriyar ta bayyana matakinta na cimma burin ganin bayan kungiyar Boko Haram. A cewar rundunar wannan gangami shi ne matakin karshe da aka sa wa suna "Operation Last Hold" da zummar murkushe sauran mayakan da ke barazana a wasu kauyuka da ke Arewa maso gabashin kasar musamman arewacin Borno da kuma wasu yankunan tabkin Chadi.

Nigeria Armee Task Force gegen Islamisten Boko Haram
Janar Tukur Buratai daga hagu da Majo janar Iliya AbbaHoto: Getty Images/AFP

Babban hafsan Sojojin kasa na Najeriya Lafatanar Janar Tukur Yusuf Buratai yace an kaddamar wannan farmaki, domin karfafa ayyukan da Sojojin ke yi a yankin arewacin Borno da bakin gabar tafkin Chadi da nufin kwato sauran wuraren da mayakan Boko Haram ke boye. Janar Buratai wanda babban kwamandan wannan runduna ta Operation Last Hold Manjo Janar Abba Dikko ya wakilta ya yi karin haske kan manufar kaddamar da wannan runduna.

Nigeria Soldaten an einem Checkpoint in Gwoza
Wata 'yar Gwoza a shingen binciken sojoji a shekarar 2015Hoto: picture-alliance/AP Photo/L. Oyekanmi

Rundunar ta ce gwamnatin tarayya za ta samar da damar yin afuwa ga mayakan da suka mika wuya tare da ajiiye makamansu. A cewar sojojin wannan gangamin karshe zai ba wa wasu kananan hukumomi damar komawa hedikwatocinsu domin ci gaba da aiki. Babban kwamandan rundunar yaki da Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya Manjo Janar Nicolas Rogers, ya nemi mutane su kwantar da hankulansu, sai dai wasu jama'ar na ganin da sauran rina a kaba ganin yadda barazanar hare-hare daga mayakan Boko Haram ke tilasta wa wasu ficewa daga yankunansu.

Rundunar sojojin Najeriyar ta ce zuwa watan Satumban shekarar 2018, mutanen da ke bakin gabar tafkin Chadi za su koma yankunansu domin ci gaba da rayuwa ba tare da fargabar hare-haren kungiyar Boko Haram ba.