Farmaki kan tsirarun addinai a Bangladesh | Labarai | DW | 03.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Farmaki kan tsirarun addinai a Bangladesh

Masu kaifin bin addini a kasar sun tarwatsa wuraren ibadan ma biya addinin Hindu mara sa rinjaye bayan zargin yin batanci ga addinin Islama inda lamarin ya shafi kimanin wuraren ibada 100 da a kauyuka tara

A cewar hukumomink asar ta Bangladesh an tura jami'an tsaro don kwatar da kura, bayan da wasu masu tsattsauran ra'ayi suka tarwatsa wuraren ibadar Hindu da ke Dhaka babban birnin kasar. Shugaban 'yan sanda a yankin da lamarin ya farau Mizanur Rahman, ya ce kawo yanzu sun dauki duk matakan kwantar da kura da ta tashi. Lamarin dai ya faro ne tun ranar Lahdin da ya gabata, bayan da aka aga wani mabiyin addinin Hindu ya a shafin Facebook ya dora hotun wani Allansu a kan dakin Ka'aba da ke Saudiyya. Hakan ya harzuka musulmai masu kaifin addini, inda suka yi ta tarwatsa wurarenn ibadar 'yan Hindu, wadanda tsiraru ne a kasar ta Bangladesh. Akalla rikichin ya sa an farma gidajen mabiya Hindu da wuraren ibada kimanin dari, kuma lamarin ya shafi kauyuka kimanin tara. Amma babban jami'an 'yan sanda ya musanta labarin, inda ya ce wuraren ibada biyar da gidaje 20 ne aka kai wa farmakin. Ministan cikin gidan Bangledash  Asaduzzaman Khan, ya ce ana tsare da mutumin da ake tuhuma da saka hotun tsokala a shafin Facebook, kuma ya bada tabbacin kare hakkin tsiraru a kasar.