1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar tashin hankali a Gabon

Gazali A/YBSeptember 12, 2016

A ranar Lahadi 11 ga watan Satumba shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika Paparoma Francis da kansa ne a cikin hudubarsa ta mako ya yi addu'a kan kasar Gabon.

https://p.dw.com/p/1K0jm
Bildkombo Ali Bongo und Jean Ping Gabon
Ali Bongo da Jean Ping 'yan siyasa biyu na Gabon da duniya ta sanya musu idanuHoto: picture-alliance/dpa/E.Laurent/L.JinMan

Batun na zaman lafiya shi ne ya kasance maudu'in da shugabannin Musulmi da kuma limaman masallatan kasar suka mayar da hankali a kai a hudubarsu ta ranar Jumma'ar da ta gabata. Ismael Oceni Ossa shi ne babban limamin masallacin Juma'a na birnin Libreville babban birnin kasar ta Gabon:

Italien Vatikan Palmsonntag Papst Franziskus
Paparoma Francis ya yi addu'a dan neman zaman lafiya a GabonHoto: picture alliance/Pacific Press Agency/G. Ciccia

"Da sunan Allah mai jin kai da rahama ina addu'a neman zaman lafiya da kwanciyar hankali da rahamar ubangiji ga kasar Gabon da al'ummarta. Wadannan tashe-tashen hankula da kashe-kashen jama'a bai dace ba ga kasar Gabon. Dangi 'yan uwa, yanzu lokaci ne na bayyana gaskiyar abin da al'umma ta zaba ta hanyar dokoki da kundin tsarin mulkin kasarmu ya tanada".

Kafin kotun tsarin mulkin ta kai ga bayyana matsayinta kan sakamakon zaben dai 'yan kasar Gabon ke rayuwa cikin fargabar da suke ta yiwuwar sake barkewar rikicin bayan zabe kamar yadda ta kasance a lokacin da ministan cikin gida ya bayyana Ali Bango a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar na ranar 27 ga watan Agusta da ya gabata. Jean Jacques Atsiba Mvou daya daga cikin limaman coci a birnin Libreville ya kira shi ma 'yan kasar zuwa ga rungumar zaman lafiya:

Gabun Libreville Ausschreitungen nach Wahlen
Matasa a kasar na dako su ji hukuncin kotu kan zaben kasarHoto: Getty Images/AFP/M. Longari

"Babu ci gaba matsawar babu zaman lafiya. Idan ba kwanciyar hankali ba za mu iya aika 'ya'yanmu makaranta ba, ko tafiya coci ko ma wurin aiki dan haka ana bukatar kwanciyar hankali a kowane fanni tun daga jiki har ruhi".

Yanzu dai 'yan kasar ta Gabon da ma sauran kasashen duniya sun kashe kunne suna sauraran sakamako da kotun tsarin mulkin kasar za ta bayyana dangane da wannan zabe wanda hukumar zaben kasar ta bayyana Ali Bango shugaba mai ci a matsayin wanda ya lashe shi abin da madugun 'yan adawar kasar Jean Ping ke da'awar shi ne ya lashe.