1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar sake barkewar yaki a Sudan ta Kudu

April 27, 2021

Wani rahoton da kwararru kan tsaro na Majalisar Dinkin Duniya suka fitar na nuni da cewa akwai yiyuwar sake barkewar wani sabon rikici a Sudan ta Kudu.

https://p.dw.com/p/3se4p
Südsudan Verhandlungen zwischen Regierung und Opposition
Hoto: Reuters/J. Solomun

Rahoton mai shafi 81 da kwararrun suka mika wa kwamitin tsaro na majalisar, ya ce bangaren mataimakin shugaban kasar Dakta Riek Machar na zargin bangaren shugaba Salva Kiir da gaza aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a bara.

Haka zalika al'umar kasar na cigaba da korafin cewa gwamnatin ta Shugaba Kiir na nuna bangaranci wajen rarraba mukamai, bayan da ya cika gwamnatin da 'yan kabilarsa ta Dimka.

Tun da fari dai mahukuntan na Sudan ta Kudu sun fuskanci matsin lamba daga kungiyoyi da kasashen ketare da a kafa gwamnatin hada ka tsakanin bangarorin da basa ga maciji da juna wanda ya baiwa Dakta Machar damar zama babban mataimakin shugaban kasa, sai dai tafiyar hawainiyar da gwamnatin ke yi na neman mayar da hannun agogo baya, yayin da lokaci da aka dibarwa cimma yarjejeniyar ke kara kurewa.