1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasa ta yi ikirarin nasara

January 19, 2021

Ana fargabar sake barkewar wani rikici a yankin Tigray duk kuwa da zaman lafiyar da aka samu.

https://p.dw.com/p/3o6mc
Äthiopien Abiy Ahme TV
Hoto: Ethiopia Broadcasting Corporation//REUTERS

Shugaba Abiy Ahmed na kasar Habasha ya ayyana nasara ga dakarun gwamnati a yakin basasar da kasar ta gwabza watanni biyu da suka gabata.

Sai dai wasu alamu na nuni da cewa akwai sauran rina a kaba, bisa la'akari da sakwannin barazana da dakarun na Tigray ke aikewa dasu a 'yan kwanakin nan.

A karshen watan Nuwamban bara ne dakarun gwamnati suka karbe Makele, birni mafi girma da masu boren ke tinkaho da shi, wanda ya tilastawa dubban mazauna yankin yin gudun hijira.