Fargaba a Kano bayan tashin bama-bamai | Siyasa | DW | 19.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fargaba a Kano bayan tashin bama-bamai

A wani hali dake kara tabbatar da yanayin rashin tsaro a Najeriya, birnin Kano ya yi Fama da tashin bama-bamai da suka haddasa rasa rayukan mutane da dama

Alkaluman lissafi sun bayyana cewar mutane 27 ne zuwa yanzu aka yi ittifakin sun rasa ransu sakamakon harin kunar bakin wake da ya afku daren jiya a unguwar Sabon Garin Kano, ko da yake a baya dai rundunar 'yan sandan jihar Kano ta jaddada cewar mutane 5 ne kawai suka rasu, sai dai wannan hari ya zama wani fami a zukatan galibin al'ummar jihar Kano, wadanda suka dauki tsawon lokaci ba tare da jin karar bam ba, lamarin da a yanzu ya kara jefa mutane cikin rudani.

Faruwar wannan hari dai ya kara sanya fargaba a cikin zukatan al'ummar jihar Kano wadanda a baya kunnuwansu suka dade da mancewa da karar fashewar bam, lamarin da a yanzu ya kara jefa su cikin fargaba. Wani abu da shima yazama tamkar wani tashin hankali shine gano wata motar kirar Mitsubishi da 'yan sandan jihar suka yi an makare ta da bama bamai, an kuma yasar da ita a titin Tafawa Balewa dake yankin Nasarawa a jihar. Wannan matsala dai tasa iyaye da dama basu tura 'ya'yansu makaranta ba a wayewar garin yau Litinin, kamar yadda wani magidanci maisuna Shehu Akai Fagge ya bayyana.

Duk cewar harin yayi kama da wanda kungiyar Jama'ati Ahalusssunah Lidda- await Waljihad da ake wa lakabi da Boko Baram ke kaiwa, amma kwamishinan 'yan sandan jihar Kano Aderinle Shinaba, ya bayyana cewar ba za a yi gaggawar cewar su suka kai harin ba, har sai abin da bincike ya nuna.

"Yace yayi wuri ace ga wanda ya kai wannan hari, amma bincike ne zai tabbatar. Haka ne ma yasa na shaida muku cewar mun fara bincike domin gano waye ya aikata, kuma binciken ne zai tabbatar mana da hakikanin gaskiya".

Tuni dai mutane suka shiga cikin halin fargaba, harma wasu suka fara zargin ko akwai siyasa a cikin harin, duba da cewar ya faru ne a daren da aka kammala fitar da sakamakon zabukan kananan hukumomi a jihar. Shemau Umar daliba ce a jihar Kano, kuma tana daga cikin masu zargin akwai alamun siyasa cikin harin.

Musa Dan Birni dattijo ne a jamiyyar PDP a jihar Kano ,wanda yace ko kadan babu ruwan jam'iyyar da wannan hari, illa dai kashin kaji da yan adawa ke shirin shafa musu.

Zuwa yanzu dai mutane sun c i gaba da gabatar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali a Kano,sai dai a wasu sassan jihar har yanzu ana zaman dar dar, musamman gano wannan mota dake makare da bama bamai.

Mawallafi: Nasiru Salisu Zango
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin