Fargaba a kan ayyukan Boko Haram | Siyasa | DW | 08.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fargaba a kan ayyukan Boko Haram

Kungiyoyin kasa da kasa na nuna damuwa da fargaba dangane da yadda kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kwace garuruwa a Tarayyar Najeriya.

A yanzu haka dai kungiyar ta Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a Tarayyar ta Najeriya na kara fadada yankunan da ke karkashinta ta hanyar kai farmaki tare da kafa tutocinta a garuruwa da kauyuka da ke jihar Borno da Adamawa, dukkansu a yankin arewa maso gabashin kasar. Kungiyoyi da ma al'umomin Najeriyar dai na nuna fargabar cewa nan ba da jimawa ba, kungiyar ta Boko Haram za ta iya kwace garin Maiduguri wanda ke zaman babban birnin jihar Borno. A tattaunawar da ya yi da tashar DW wani jami'in kungiyar kasa da kasa da ke sulhunta rikice-rikice Nnamdi Obasi ya ce tabbas akwai yiwuwar nan ba da jimawa ba Boko Haram za ta kwace Maiduguri inda ya ce.....

"In har hakan ta faru zai zama wani babban koma baya ga gwamnati da kuma gazawar jami'an tsaro na yakar 'yan ta'addan sai dai ba zai zamo faduwar yankin baki daya nan take ba sai dai zan janyo fargaba da za ta haifar da asarar rayuka masu yawa"

Nigeria Flüchtlinge in Maiduguri

Jama'a na gudun hijira Domin tsira da ransu

Obasi ya ce in har aka kyale kungiyar za ta yi kokarin ci gaba da kwace garuruwa tamkar yadda kungiyar IS ke yi a yanzu haka a Iraki. A yanzu haka dai kungiyar ta Boko Haram ta fadada hare-haren da ta ke kaiwa jihar Adamawa inda ta kwace garuruwa da dama da suka hadar da Michika da Gulak da Madagali. Wani mazaunin garin Michika na jihar Adamwan da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro ya ce yanzu haka garin Mubi ma ya fara zama tamkar kushewa domin kuwa kowa ya tsere don ya tsira da ransa.

Mutane na fama da yunwa

Ya kara da cewa suna zaune ne cikin tashin hankali da fargaba domin kuwa babu shaguna haka nan ma kasuwanni a rufe suke. Ya ce garin kwaki da kuli-kuli da suka dan yi guzurinsa suke ci in kuma ya kare basu san yadda za su yi ba. Shin ko yana ganin 'yan ta'addan na Boko Haram ka iya hada yankunan da suka kwace a Adamawan da wadanda suka kwace a jihar Borno wajen fadada daular da suka yi ikirarin kafawa? A cewarsa in har aka ci gaba da tafiya a haka to tabbas duk garin da suka zo suka iske babu kowa za su kafa tutocinsu ne tare da hakimcewa a matsayin mahukuntan wanna gari.

Nigeria Soldaten Archiv 2013

Sojojin Najeriya a bakin aiki

Babban abun damuwar ko kuma abun tambaya dai shi ne yadda 'yan kungiyar ta Boko Haram ke amfani da hanyoyin garuruwan da suka kwacewa wajen shiga a nutse ta re da kai farmaki wanda kuma ke basu nasarar kame garuruwan. Nnamdi Obasi na kungiyar kasa da kasa da ke sulhunta rikice-rikice ya shaidawa tashar DW cewa....

Yaki ne mai tsauri da rikitarwa

"Jami'an tsaron na fuskantar babban kalubale wajen yakar 'yan ta'addan, suna da hikimomin da suke amfani da su wajen dauke hankulan jami'an tsaro kafin su kaddamar da kai hare-hare. Yaki ne mai tsauri da kuma rikitarwar gaske."

Nnamdi Obasi ya ce akwai bukatar sake zage damtse wajen yakar 'yan kungiyar ta Boko Haram ta hanyar taimako daga kasa da kasa musammnma kasashen da suka hada iyaka da Najeriya wato kamar Kamaru da Chadi, sannan kuma jami'an tsaro su sake dagewa wajen ganin al'ummomin yankin sun aminta da su kasancewar suma suna da na su matsalolin dangane da yadda suke gudanar da ayyukansu. Ya ce akwai bukatar ita kanta gwamnati ta kara inganta ayyukan jami'an tsaron nata ta yadda za su iya fafatwa da 'yan ta'addan.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita:Pinado Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin