1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farfadowar harkokin yawon bude ido a Masar

Zulaiha Abubakar
July 1, 2020

Gwamnatin kasar Masar ta sanar da bude gidajen adana kayan tarihi da kuma fitaccen wurin yawon bude ido na Giza a karon farko bayan tsawon watanni.

https://p.dw.com/p/3ediE
Ägypten Gizeh Touristen besuchen Pyramiden
Hoto: picture-alliance/dpa/K. El-Fiqi

Wannan sanarwa ta fito bayan kamfanin jiragen saman kasar Egypt Air ya bayyana cewar akalla fasinjoji dubu biyu ne suka yi tafiya daga filin jirgin saman Masar zuwa kasashen ketare 14 a wannan Larabar. Sakataren hukumar adana kayan tarihi da yawon bude ido a Masar Mostafa Waziri, ya tabbatarwa da manema labarai cewar wasu tagwayen jiragen sama dauke da fasinjoji 350 'yan yawon bude ido daga kasar Ukraine sun sauka a Kudancin kasar.

Bugu da kari gomman gidajen adana kayan tarihi na karbar masu ziyara a kowacce rana duk da irin tsauraran matakan kariya daga cutar coronavirus da mahukuntan kasar suka kaddamar, wannan ci gaba a harkokin bude ido na nunar da alamun nasara a aikin da gwamnatin kasar ta dauki lokaci tana yi na farfado da bangaren yawon bude ido da shakatawa a Masar.